Rivers: Wike ya haramta karuwanci a kan titi,
Rivers: Wike ya haramta karuwanci a kan titi,
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sanya dokar hana karuwanci a tituna da gidajen dare a wasu sassan birnin Fatakwal.
Wike, wanda ya bayyana hakan a wani watsa shirye-shiryen sabuwar shekara a ranar Asabar, ya ce an dauki matakin ne don dakile baje koli da neman yin jima'i, shan muggan kwayoyi da kuma sa maye da ke faruwa a kan titunan da wuraren jama'a.
Don haka, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirga cikin gaggawa a duk wasu harkokin gidajen rawa da suka hada da sana’ar dare da karuwanci a kan titin Abacha da kewayen titunan domin dakile illolin da wadannan miyagun ayyuka ke haifarwa ga ci gaban tarbiyyar ‘ya’yanmu da sauran al’umma baki daya. "in ji Wike.
Comments
Post a Comment