Posts

ATIKU YA KOKA DA HALIN DA NIGERIA TAKE CIKI

Image
  Ba a taba ba: Atiku ya shiga damuwa, ya ce bai taba ganin irin matsalar da Najeriya ke ciki ba. Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya koka da kalubalen da Najeriya ke fuskanta a yanzu. A cewar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kasar nan ba ta taba samun kanta a irin wannan matsala mara kan gado ba.  Abubakar ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa na Daily Trust karo na 19 da ke gudana a dakin taro na NAF Conference Centre and Suites, dake kan titin Gwarinpa, kusa da NEXT Shopping Mall, Kado da ke Abuja.  Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya koka da kalubalen da Najeriya ke fuskanta a yanzu. A cewar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kasar nan ba ta taba samun kanta a irin wannan matsala mara kan gado ba.  Abubakar ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa na Daily Trust karo na 19 da ke gudana a dakin taro na NAF Conference Centre and Suites, dake kan titin Gwarinpa, kusa da NEXT Shopping Mall, Kado da ke Abuja...

Yanzu-Yanzu: Sojojin Najeriya sun halaka Alhaji Auta, riƙaƙƙen ɗan fashin dajin da ya addabi Zamfara

Image
 Yanzu-Yanzu: Sojojin Najeriya sun halaka Alhaji Auta, riƙaƙƙen ɗan fashin dajin da ya addabi Zamfara Dakarun sojin Najeriya sun hallaka wasu riƙaƙun ƴan fashin daji biyu da suka addabi jihar Zamfara da maƙwabtatanta da suka haɗar da Kachalla Ruga da kuma Alhaji Auta. Jaridar PrNigeria ta rawaito cewa mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne yayin luguden wutar jiragen sojin saman Najeriya a wasu dazuka da ke ƙauyen Gusami da kuma kauyen Tsamre a karamar hukumar Birnin Magaji. Kafin mutuwarsu dai suna cikin gawurtattun ƴan fashin dajin da suka addabi arewa maso yammacin Najeriya. Wasu majiyoyi sun ce an kuma hallaka yaransu da dama a lokacin hare-haren.

KWANKWASO ZAI KOMA APC TAREDA MA GOYA BAYANSA

Image
  Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kusa kammala shirinsa na komawa jam’iyyar APC. Kwankwaso, wanda tsohon Sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, bai ji dadin jam’iyyar PDP ba tun bayan tarzomar da aka yi a babban taron jam’iyyar a watan Afrilu a Kaduna. Taron wanda ‘yan Kwankwasiyya suka tarwatsa, ya biyo bayan ganin cewa dan takarar su na kujerar mataimakin shugaban Jam’iyyar ba zai yi nasara ba. Sanata Kwankwaso wanda ke goyon bayan Mohammed Jamo Yusuf kan Bello Hayatu Gwarzo, ya dage cewa a bar shi ya kawo mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin daga bangarensa. Sanata Bello Hayatu Gwarzo yana samun goyon bayan mafi rinjayen masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso Yamma da suka hada da Gwamna Aminu Tambuwal, wanda Kwankwaso daman ya zarge shi da shine ya sayawa Bello Hayatu form din takarar a wata hira da BBC tai da kwankwason Bayan kammala taron da ba a yi shi ba saboda tarzoma, da kuma ganin yadda Kwankwaso ya sha kaye, ya tabbatar ...

Mu na da hujja a kan rufe sansanin ‘yan gudun hijira – Zulu

Image
  Mu na da hujja a kan rufe sansanin ‘yan gudun hijira – Zulum Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce, an rufe dukannin sansanonin ƴan gudun hijira da ke jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a saƙon murnar sabuwar shekara da ya fitar, inda ya ce, matakin da a ka ɗauka na rufe dukannin sansanonin an ɗauke shi ne, domin ƙara inganta rayuwar jama’a. A makon da ya gabata, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun roƙi hukumomi da su janye wannan kudirin na su, sakamakon gwamnati ba ta da tabbaci na kula da haƙƙoƙin ƴan gudun hijira. Ƙungiyoyin sun yi gargaɗin cewa, yunƙurin da a ke yi na mayar da ƴan gudun hijira muhallansu zai sa rayukan sama da iyalai 10,000 cikin hatsari, sakamakon irin hare-haren da ƴan Boko Haram da ƴan ISWAP ke ci gaba da kai wa da kuma zargin cin zarafi da sojoji ke yi. Sai dai Gwamna Zulum ya dage kan cewa, sansanonin sun soma zama wurare da ake aikata munanan abubuwa iri-iri, ciki har da karuwanci da sayar da miyagun ƙwayoyi da kuma daba a wasu lokutan. BBC ...

Rivers: Wike ya haramta karuwanci a kan titi,

Image
  Rivers: Wike ya haramta karuwanci a kan titi,  Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sanya dokar hana karuwanci a tituna da gidajen dare a wasu sassan birnin Fatakwal. Wike, wanda ya bayyana hakan a wani watsa shirye-shiryen sabuwar shekara a ranar Asabar, ya ce an dauki matakin ne don dakile baje koli da neman yin jima'i, shan muggan kwayoyi da kuma sa maye da ke faruwa a kan titunan da wuraren jama'a. Don haka, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirga cikin gaggawa a duk wasu harkokin gidajen rawa da suka hada da sana’ar dare da karuwanci a kan titin Abacha da kewayen titunan domin dakile illolin da wadannan miyagun ayyuka ke haifarwa ga ci gaban tarbiyyar ‘ya’yanmu da sauran al’umma baki daya. "in ji Wike.

Kin saka wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe hannu da Buhari ya yi rahama ce ga talakawan Najeriya – Garba Shehu

Image
  Kin saka wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe hannu da Buhari ya yi rahama ce ga talakawan Najeriya – Garba Shehu Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya bayyana cewa makudan kudin da za a kashe wajen gudanar da zaben a kasar nan zai wuce misali idan har shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu a kudirin gyaran dokar zabe da majalisa suka aika masa. Shehu yace ganin irin wannan makudan kudade ne da za akashe ya sa shugaba Buhari ya maida wa majalisa da wannan kudiri cewa ba zai sanya mata hannu. ” Makudan kudaden da za a kashe a wurin gudanar da zabe musamman a wannan lokaci shine tashin hankali, domin kawai a gudanar da zabe. Maimakon haka aiki na ci gaba ya kamata ace an yi da su ba narka su a wajen zabe bakawai . ” Da farko dai kudin talakawa za anarka, kuma daga karshe masu kudi yan siyasa ne za su amfana da shi. Tsakani da Allah ba wannan lokaci bane Najeriya za ta yi gangancin narka kudi a siyasa kawai don amfanin wasu ba talakawa ba. ” A tuna fa a yanzu haka ma gwagwagwa ak...