Posts

Showing posts from January, 2022

ATIKU YA KOKA DA HALIN DA NIGERIA TAKE CIKI

Image
  Ba a taba ba: Atiku ya shiga damuwa, ya ce bai taba ganin irin matsalar da Najeriya ke ciki ba. Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya koka da kalubalen da Najeriya ke fuskanta a yanzu. A cewar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kasar nan ba ta taba samun kanta a irin wannan matsala mara kan gado ba.  Abubakar ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa na Daily Trust karo na 19 da ke gudana a dakin taro na NAF Conference Centre and Suites, dake kan titin Gwarinpa, kusa da NEXT Shopping Mall, Kado da ke Abuja.  Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya koka da kalubalen da Najeriya ke fuskanta a yanzu. A cewar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kasar nan ba ta taba samun kanta a irin wannan matsala mara kan gado ba.  Abubakar ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa na Daily Trust karo na 19 da ke gudana a dakin taro na NAF Conference Centre and Suites, dake kan titin Gwarinpa, kusa da NEXT Shopping Mall, Kado da ke Abuja...

Yanzu-Yanzu: Sojojin Najeriya sun halaka Alhaji Auta, riƙaƙƙen ɗan fashin dajin da ya addabi Zamfara

Image
 Yanzu-Yanzu: Sojojin Najeriya sun halaka Alhaji Auta, riƙaƙƙen ɗan fashin dajin da ya addabi Zamfara Dakarun sojin Najeriya sun hallaka wasu riƙaƙun ƴan fashin daji biyu da suka addabi jihar Zamfara da maƙwabtatanta da suka haɗar da Kachalla Ruga da kuma Alhaji Auta. Jaridar PrNigeria ta rawaito cewa mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne yayin luguden wutar jiragen sojin saman Najeriya a wasu dazuka da ke ƙauyen Gusami da kuma kauyen Tsamre a karamar hukumar Birnin Magaji. Kafin mutuwarsu dai suna cikin gawurtattun ƴan fashin dajin da suka addabi arewa maso yammacin Najeriya. Wasu majiyoyi sun ce an kuma hallaka yaransu da dama a lokacin hare-haren.

KWANKWASO ZAI KOMA APC TAREDA MA GOYA BAYANSA

Image
  Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kusa kammala shirinsa na komawa jam’iyyar APC. Kwankwaso, wanda tsohon Sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, bai ji dadin jam’iyyar PDP ba tun bayan tarzomar da aka yi a babban taron jam’iyyar a watan Afrilu a Kaduna. Taron wanda ‘yan Kwankwasiyya suka tarwatsa, ya biyo bayan ganin cewa dan takarar su na kujerar mataimakin shugaban Jam’iyyar ba zai yi nasara ba. Sanata Kwankwaso wanda ke goyon bayan Mohammed Jamo Yusuf kan Bello Hayatu Gwarzo, ya dage cewa a bar shi ya kawo mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin daga bangarensa. Sanata Bello Hayatu Gwarzo yana samun goyon bayan mafi rinjayen masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso Yamma da suka hada da Gwamna Aminu Tambuwal, wanda Kwankwaso daman ya zarge shi da shine ya sayawa Bello Hayatu form din takarar a wata hira da BBC tai da kwankwason Bayan kammala taron da ba a yi shi ba saboda tarzoma, da kuma ganin yadda Kwankwaso ya sha kaye, ya tabbatar ...

Mu na da hujja a kan rufe sansanin ‘yan gudun hijira – Zulu

Image
  Mu na da hujja a kan rufe sansanin ‘yan gudun hijira – Zulum Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce, an rufe dukannin sansanonin ƴan gudun hijira da ke jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a saƙon murnar sabuwar shekara da ya fitar, inda ya ce, matakin da a ka ɗauka na rufe dukannin sansanonin an ɗauke shi ne, domin ƙara inganta rayuwar jama’a. A makon da ya gabata, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun roƙi hukumomi da su janye wannan kudirin na su, sakamakon gwamnati ba ta da tabbaci na kula da haƙƙoƙin ƴan gudun hijira. Ƙungiyoyin sun yi gargaɗin cewa, yunƙurin da a ke yi na mayar da ƴan gudun hijira muhallansu zai sa rayukan sama da iyalai 10,000 cikin hatsari, sakamakon irin hare-haren da ƴan Boko Haram da ƴan ISWAP ke ci gaba da kai wa da kuma zargin cin zarafi da sojoji ke yi. Sai dai Gwamna Zulum ya dage kan cewa, sansanonin sun soma zama wurare da ake aikata munanan abubuwa iri-iri, ciki har da karuwanci da sayar da miyagun ƙwayoyi da kuma daba a wasu lokutan. BBC ...

Rivers: Wike ya haramta karuwanci a kan titi,

Image
  Rivers: Wike ya haramta karuwanci a kan titi,  Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sanya dokar hana karuwanci a tituna da gidajen dare a wasu sassan birnin Fatakwal. Wike, wanda ya bayyana hakan a wani watsa shirye-shiryen sabuwar shekara a ranar Asabar, ya ce an dauki matakin ne don dakile baje koli da neman yin jima'i, shan muggan kwayoyi da kuma sa maye da ke faruwa a kan titunan da wuraren jama'a. Don haka, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirga cikin gaggawa a duk wasu harkokin gidajen rawa da suka hada da sana’ar dare da karuwanci a kan titin Abacha da kewayen titunan domin dakile illolin da wadannan miyagun ayyuka ke haifarwa ga ci gaban tarbiyyar ‘ya’yanmu da sauran al’umma baki daya. "in ji Wike.

Kin saka wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe hannu da Buhari ya yi rahama ce ga talakawan Najeriya – Garba Shehu

Image
  Kin saka wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe hannu da Buhari ya yi rahama ce ga talakawan Najeriya – Garba Shehu Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya bayyana cewa makudan kudin da za a kashe wajen gudanar da zaben a kasar nan zai wuce misali idan har shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu a kudirin gyaran dokar zabe da majalisa suka aika masa. Shehu yace ganin irin wannan makudan kudade ne da za akashe ya sa shugaba Buhari ya maida wa majalisa da wannan kudiri cewa ba zai sanya mata hannu. ” Makudan kudaden da za a kashe a wurin gudanar da zabe musamman a wannan lokaci shine tashin hankali, domin kawai a gudanar da zabe. Maimakon haka aiki na ci gaba ya kamata ace an yi da su ba narka su a wajen zabe bakawai . ” Da farko dai kudin talakawa za anarka, kuma daga karshe masu kudi yan siyasa ne za su amfana da shi. Tsakani da Allah ba wannan lokaci bane Najeriya za ta yi gangancin narka kudi a siyasa kawai don amfanin wasu ba talakawa ba. ” A tuna fa a yanzu haka ma gwagwagwa ak...

Zamfara: ‘Yan sanda sun ceto yara 21 daga ‘yan ta’adda

Image
  Zamfara: ‘Yan sanda sun ceto yara 21 daga ‘yan ta’adda Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta ceto ƙananan yara 21, ciki har da mata biyu waɗanda ke hanyarsu ta zuwa wata makarantar Islamiyya ta Almajirai da ke Katsina. A wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu ya fitar, sanarwar ta ce, yaran sun taso ne daga ƙauyen Rini da ke Ƙaramar Hukumar Bakura ta jihar Zamfara. Tun da farko jami’an tsaron sun samu labarin cewa, ƴan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa Funtua ta ɓangaren Kucheri, inda su ka yi garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba daga motoci biyar. Hakan ya sa jami’an suka nufi wurin inda su ka yi bata-kashi da ƴan bindigan. Ƴan sandan Zamfaran dai sun yi kira ga musamman direbobi da fasinjoji da su kiyayi tafiyar dare, inda su ka ce akasari da dare ne ɓarayi ke tare hanya.

Buhari ya ce ko sisin kobo mutum ya ci sai ya amayar kuma a ɗaure shi

Image
  Buhari ya ce ko sisin kobo mutum ya ci sai ya amayar kuma a ɗaure shi BINCIKEN TATSAR HANJIN HUKUMAR NDDC:   Buhari ya ce ko sisin kobo mutum ya ci sai ya amayar kuma a ɗaure shi Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana da kakkausan harshe cewa dukkan waɗanda su ka ci kuɗaɗen Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta (NDDC) sai sun amayar da su kuma za a hukunta su. Buhari ya bayyana haka a Jihar Akwa Ibom, a lokacin da ya ke buɗe wani katafaren ginin ɗakin kwanan ɗalibai a Jami’ar Uyo. “Bari na sanar da ku cewa duk waɗanda su ka ci kuɗin da aka ware domin inganta rayuwar al’ummar Neja Delta, sai sun amayar da kuɗaɗen. Kuma za a hukunta su.” Haka Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa Femi Adesina ne ya bayyana haka a ranar Alhamis. Tuni dai Buhari ya bada umarnin a gudanar da binciken ƙwaƙwaf a NDDC, bayan samun rahoton cewa an yi shagalin da kuɗaɗen hukumar ta NDDD. PREMIUM TIMES Hausa ta taɓa buga labarin yadda aka riƙa watandar maƙudan biliyoyin kuɗaɗe a NDDC. An kuma gano yadda aka...

Nan gaba za a rubuta sunayen mu da alƙalamin zinari – Buhari

Image
    Nan gaba za a rubuta sunayen mu da alƙalamin zinari – Buhari Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk da matsaloli da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, ya na da yaƙinin cewa nan gaba za a yaba masa dangane da irin ayyukan da ya samar, ta yadda a cewar sa za a rubuta “sunayen mu da alƙalamin zinari.” Cikin jawabin wanda ya fitar a ranar Juma’a daga Fadar Shugaban Ƙasa, Buhari ce ya na yi wa sabuwar shekarar 2022 marhabin, cike da fatan cewa wannan shekara za ta ɗara ta 2021 wajen samar da ci gaba, tsaro da inganta tattalin arziki. “Duk da cewa mun fuskanci ƙalubale masu yawa cikin 2021, to an yi ayyukan raya ƙasa, an samar da ababen inganta rayuwar talakawa da kuma ayyukan inganta tattalin arzikin ƙasa. “Mun maida hankali sosai wajen ganin mun cika alƙawarin nan uku na samar da tsaro, inganta tattalin arziki da kuma yaƙi da rashawa da zambar kuɗaɗe. “Tabbas mun ci karo da matsaloli da ƙalubale, musamman ɓarkewar cutar korona, wadda ta dakushe kaifin tattalin arzikin Na...

Gagarumin abun al'ajabi ne da mu'ujiza tsira a karkashin mulkin Buhari, PDP

Image
  Gagarumar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta taya 'yan Najeriya murnar zuwan sabuwar shekarar 2022. A sakon murnar sabuwar shekarar da jam'iyyar PDP ta fitar ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Honarabul Debo Ologunagba, ta yi kira ga 'yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokacin wurin farfado da soyayya, haduwar kai, adalci tare da bukatar samun shugabanci nagari a kasar nan. Jam'iyyar ta ce tsira a shekarar 2021 karkashin mulkin All Progressives Congress (APC) ba tuna baya kadai ya dace a yi ba, ya dace a hada da kokarin ganin cewa an ceto kasar nan daga mulkin kama karya. Ya ce abun al'ajabi ne yadda kasar nan ta kwashe shekaru shida cikin "take hakkin dan Adam, kashe-kashe ba tare da yanke hukunci ba, rashin ababen more rayuwa, tsanani a fannin tattalin arziki, hauhawar ta'addanci da kuma kashe mutane wanda duk aka samu sanadiyyar mulkin APC."

ALAMOMI 10 GA WANDA DUNIYA TA AURE SHI

1. Idan ya zamto baka jiran sallah saidai sallah ta jiraka. 2. Idan ya zamto kwana biyu zuwa uku baka bude Qur'anin ka ba (wai bakada lokaci). 3. Idan ya zamto kafi damuwa daka burge mutane koda zaka sabawa ubangijinka. 4. Idan ya zamto kullum tunaninka yaddazakayi ka tara dukiya da kudi bakada lokacin tunanin hisabi. 5. Idan ya zamto baka karbar nasiha.  6. Idan ya zamto babu rayuwar da take birgeka sai rayuwar mawaka da 'yan kwallo da makada. 7. Idan ya zamto bakada lokacin sauraron wa'azi ko karatun al-qur'ani.   8. Idan ya zamto kana jinkirta aikin alkheri sai watarana. 9. Idan ya zamto bakada lokacin neman ilmin addininka sai dai na neman duniya (boko). 10. Idan ya zamto ka karanta wannan sakon ba tare da kayi Share dinsa ba don 'Yan'Uwa su Amfana, kuma bai Qareka da komae ba. Allah (swt) Ya Yafe mana zunuban mu manya da qanana Ameen Summa Ameen.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya kuma bada shawara ga mutanensa su nemi makamai

Image
  Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya kuma bada shawara ga mutanensa su nemi makamai Rt. Hon. Masari yace ba zai yiwu jama’a su zauna haka kurum ana kawo masu hari ba su da bindiga ba Gwamnatin Masari za ta taimaka wajen ganin an yi wa duk bindigogi lasisi domin gudun a samu matsala.  Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya yi kira ga mazauna su nemi bindigogi domin su iya kare kansu da miyagun ‘yan bindiga. Jaridar Premium Times ta rahoto Aminu Bello Masari ya na wannan kira ne saboda jami’an tsaro kadai ba za su iya magance matsalar rashin tsaro a Katsina ba. Da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati na Muhammadu Buhari da ke birnin Katsina, gwamnan yace jami’an tsaron da ke jihar sun yi kadan. READ ALSO Ku sayi bindiga, ku kare kan ku: Masari ya yi kira ga al'ummar jiharsa Kamar yadda Premium Times ta fitar da rahoto a ranar 29 ga watan Disamba, 2021, Aminu Masari yace duk wanda ya mutu wajen kare kan shi, to ya yi shahada. Masari ...